Hukumar kula da yanayi ta Amurka, ta yi gargadin cewa, za a fuskanci matsanancin zafi mai cike da hadari a wannan karshen makon da ake ciki, wanda zai iya haifar da matsananciyar gajiya da za ta sa har mutum ya fita a hayyacinsa, muddin jama'a ba su bi matakan da suka dace ba.
Hukumar ta kuma ba da shawara ga ‘yan uwa da makwabta da abokanai, da su rika duba halin da junansu ke ciki, musamman ma gajiyayyu da ke zaune a daki ba sa iya fita, domin sanin halin da suke cike.
“Zafi shi ne babban abin da ya fi kisa a yanayi daban-daban da ake da su, yana kisa fiye da mahaukaciyar guguwa da ambaliyar ruwa.” Inji Andrew Grunstein, malami a sashen nazarin mahangar taswirar fadin duniya, wato Geography, a jami’ar Georgia da ke nan Amurka.
A 'yan kwanakin nan, yanayi na zafi ya karu matuka a biranen da ke yammcin tsakiya da kuma gabashin Amurka.
Hukumomin birane sun ba da umurnin a bar tafkunan ninkaya su kasance a bude na tsawon lokutan da suka dara na da, tare da aikewa da sakonnin matakan da mutane ya kamata su dauka domin magance wannan zafi mai tsanani.
Makin zafin ya kai 38 Washington, babban birnin Amurka sannan ya kai 33 a birnin New York duk a mataki na ma’aunin Celcius.