Nijar: An Kama Ministan Watsa Labarai Mahamadou Zada Saboda Zargin Karkata Akalar Wasu Kudade

Mahamadou Zada

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun cafke ministan watsa labaran kasar Mahamadou Zada saboda zarginsa da yin rub da ciki akan dubban miliyoyin cfa a zamanin da ya ke rike da mukamin babban Darektan  kamfanin dillancin ma’adanai SOPAMIN.

Tuni wannan mataki ya fara haifar da mahawara a tsakanin jama’a.

Mahamadou Zada wanda ya shafe darensa na farko a gidan yarin Kollo dake a tazarar kilomita 30 da birnin Yamai ya shafe awoyi yana amsa tambayoyin alkali mai bincike a jiya Talata.

Ana tuhumarsa ne wawure wasu kudade milliyoin 3,000 na cfa da ake zargin ya batar a lokacin da yake rike da mukamin babban darektan kamfanin dillancin ma’adanan karkashin kasa wato SOPAMIN mallakar gwamnati.

Matakin da shugaban kungiyar yaki da cin hanci Transparency Interantional reshen Nijar Malan Maman Wada ke dauka a matsayin babban ci gaba a wannan fanni.

Shi ma mataimakin shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula na FSCN Abdou Elhadji Idi ya yaba da abinda ya kira babban hobbasa a farautar mahandama dukiyar kasa.

Sai dai dukkan wadanan malamai sun yi amanna akan bukatar daukan matakan kaucewa tarnakin da aka saba fuskanta a can baya a yayin bayyanar makamantan wannan badakala.

A bara ne rikici ya barke a tsakanin babban darektan kamfanin SOPAMIN Mahamadou Zada da shugaban bankin talakkawa TAANADI SA, bayan da ya ce ya yi ajiyar miliyon 3000 na cfa da sunan kamfanin na dillancin ma’adanai yayin da shugaban bankin ya ce sam bai ga takardun ajiyar wadanan kudade ba.

Hakan ya sa aka kaddamar da binciken da a watannin baya ya janyo kulle shugaban TAANADI a kurkuku.

Sai ga shi kuma matakin zurfafa bincike ya rutsa da Mahamadou Zada mai rike da mukamin ministan watsa labarai a gwamnatin kawancen da yake wakiltar jam’iyar MPR Jamhuriya.

Alhaji Assoumana Mahamadou shi ne kakakin PNDS Tarayya ya kuma ce duk wanda ya aikata laifin, ko shi wane ne, za su shiga wando daya da shugaban kasa.