Hukumomi Sun Cafke Wani Malamin Addinin Islama Saboda Zarginsa Da Auren Mata 78

Rundunar yan sanda

Hukumomin jamhuriyar Nijer sun kama wani malamin addinin Islama da ake kira Gausu Al-Mustapha, sakamakon zargin aikata wasu manyan laifuka ciki har da auren gomman mata.

Sheik Al-Moustapha Aboubacar wanda ke zaune a kauyen Tudun Fela na gundumar tsibirin Dogon doutsi, mashahurin malamin Islama ne da ke da dimbin jama’a, a makon jiya ne labarin kama shi ya bayyana a lokacin da aka gabatar da shi a gaban alkalin kotun kula da laifukan da ke da nasaba da ta’addanci, duk kuwa da cewa ya shafe watanni a kalla biyu a ofishin jami’an tsaron jandarma.

Malamin da ke auren mata 78 na fuskantar tuhumar aikata wasu laifukan da suka saba wa addini a gefe daya kuma suka take dokokin kasa da kasa.

Ousman Tahirou, wanda Daya ne daga cikin tsofaffin almajiran wannan malami, yace kosawa da abubuwan da jagoran nasu ke aikatawa ne ya sa jama’a soma bijire wa umurninsa har aka kai matsayin da labarin ya isa kunnuwan mahukunta.

Yunkurin jin ta bakin almajiran Gausu Almustapha da danginsa ya ci tura.

Bayan ayyukan yada addini malamin da ke kiran kansa Mahadi na ayyukan noma, inda almajirai da mukarrabansa ke aiki tukuru domin samar da cimakar da yake ciyar da su.

Kawo yanzu dai ba a yi zaman shari’arsa ba ballantana a iya sanin abinda ka iya zama makomarsa.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomi Sun Cafke Wani Malamin Islama Saboda Zargin Auren Mata 78