Jami'an Amurka Na Binciken Mutuwar Shugaban 'Yan Adawar Zimbabwe

Roy Bennett Da Matar Shi

Shugaban 'yan rajin kwarzabar gwamnatin tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe mai suna Roy Bennett ya mutu tare da matarsa a wani hatsarin jirgin sama.

Hukumomin Amurka suna binciken hadarin jirgin nan wanda yayi sanadiyyar mutuwar babban shugaban adawa na kasar Zimbabwe Roy Bennett da matarsa tare da wasu mutane uku.

'Yan sanda sunce jirgin ya fadi ne a daren ranar Laraba a wani wuri mai tsaunuka da ke lungu a jihar New Mexico da ke Kudu maso Yammacin Amurka, kusa da kan iyakar jihar Colorado.

Wani fasinja da ya ji ciwo a hadarin shine yayi kiran neman taimako. Babu masaniyar hakikanin abinda Bennett tare da matarsa suka je yi a New Mexico.

A lokacin da Bennett dan shekaru 60 yake raye, ya kasance dan rajin dake taimakawa talakawa da adawa mai zafi ga tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, wanda aka tilastawa sauka daga mulki a shekarar data gabata.