Hukumomin jamhuriyar Niger suna Fadakar da Jama’a Akan Kasafin Kudin Kasar

Shugaban Jamhuriyar Niger Issoufou Mahammadou

Makon da ya gabata ne gwamnatin Nijar ta fitar da kasafin kudinta na shekarar 2018 tare da dokar dorawa kudin gado haraji abun da wasu a kasar suka ce basu amince ba.

Yanzu haka dai hukumomin jihohi da gundumomi da kananan hukumomi suna ci gaba da gudanar da tarruruka da zummar fadakar da al’ummar kasar gameda tsarin kasafin kudin na shekara mai zuwa.

Tarrurukan sun hada da sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa da kungiyoyin farar hula da kungiyoyin ma’aikata da shugabannin rundunonin tsaro. Haka ma an gaiyato matasa da manoma da kuma makiyaya zuwa garin Birnin Konni.

Magajin garin Konni da ya halarci taron ya gargadi mahalarta taron akan kiyaye tashin hankali saboda idan an san farkonsa ba za’a san karshensa ba. Yace lallai lokacin da kasafin kudin ya fito an sha cece kuce akansa amma ya kamata a kawowa juna fahimta musamman abun da ya shafi rabon gado. Yace sun zauna kuma sun bayyana masu abun da gwamnati ke nufi. Yanzu sun gane abubuwan da ake fadi ba haka suke ba.

Gwamnatin kasar ce ta ba da umurnin a tara mutane domin a fadakar daal’umma akan kasafin kudin kamar yadda magatakardan Konni ya bayyana.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin jamhuriyar Niger suna Fadakar da Jama’a Akan Kasafin Kudin Kasar - 3' 31"