Duk da buga labarin da kafafen yada labarai su ka yi cewa, ana jan kafa wajen soma ayyukan hada kundin rajistar masu kada kuri’a a zabukan 2021 na kasar, lamarin da suka ce na damin gwamnatin Nijar wace, ta hanyar Ministan Cikin Gidan kasar ta ja hankulan shuwagabanin kamfanin kasar Faransa da ke aikin, akan bukatar su farga daga barci, mafari kenan da bangarorin biyu suka kira taron manema labarai, don fitar da jama’a daga duhu.
Aladoua Amada, Mataimakin Shugaban Hukumar Zaben Nijar (CENI a takaice) ya jaddada cewa wannan al’amari ne mai matukar sarkakkiya, saboda haka ya kamata kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki su bi a hankali. Ya ce hukumar na bukatar mutum dubu bakwai baya ga sauran bukatun da Nijar ba ta da kwarewa a kai, wanda don haka ne ma aka tuntubi kamfanin da ya kware.
Shi ma Wakilin kamfanin Gemalto na kasar Faransa Jean Michel ya bada tabbacin cewa komai zai gudana akan lokacin da aka tsayar, saboda haka batun saba alkawali bai ma taso ba a bisa la’akari da irin darussan da suka koya a yayin gudanar da irin wadanan aiyuka a kasashe da dama na Afirka.
Milliard ko billion 20 na cfa ne ake bukata domin gudanar da aikin hada wannan kundi da ake ganin zai taimaka a toshe dukkan wata kafar magudin zaben. A ra’ayin wasu ‘yan kasar rashin cika alkawali daga bangaren Nijar ne ya haddasa tsaiko wajen soma wannan aiki abinda hukumar zaben kasar tace ba gaskiya ba ne.
Ga dai wakilinmu Sule Barma da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5