Hukumar Zaben Najeriya Ta Yi Alkawarin Gudanar Da Ingantace Zabe Badi

Farfesa Mahmoud Yakubu shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC

A jihar Oyo hukumar zabe ta yi taron fadakar da jama’a akan mahimmancin mallakar katin zabe na din din din saboda shi ne kadai makamin jefa kuri’a a kowane zabe tare da bada tabbacin gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa

Hukumar zaben Najeriya, INEC ta yi alkawarin gudanar da sahihin zabe kuma mai inganci a zaben shekarar 2019 da za’a yi a kasar.

Kwamishanan zabe mai kula da jihar Oyo shi ya sanar da hakan a lokacin wani taron wayar da kawunan jama’a dangane da yin anfani da katin zabe.

Inji kwamishanan sun lashi takobin gudanar da ingantace zabe domin tuni suka fara sake horas da jami’ansu dangane da zabukan shekar mai zuwa. Ya ce hukumar ba zata yi wani mirsisi ba a lokacin zabukan.

Kwamishanan ya sanar ce har yanzu akwai katukan zabe na din din din fiye da dubu dari biyu na wasu mutane kuma ya bukacesu su yi kokarin zuwa karbansu domin su yi anfani dasu a lokutan zabe.

Sai dai kwamishanan ya musanta rade-radin cewa hukumar zata kara sabbin mazabu a duk fadin Najeriya.

Ita ko daraktar wayar da kawunan jama’a a jihar Uwargida Dolapo Dosumu ta ce an shirya taron ne domin ilmantar da jama’a akan mahimmancin katin zabe domin shi ne kadai makamin yin zaben.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Zaben Najeriya Ta Yi Alkawarin Gudanar Da Ingantace Zabe Badi – 2’ 18”