Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Najeriya, Ta Fara Shirin Kiranyen Sanata Dino Melaye


Sanata Dino Melaye
Sanata Dino Melaye

Sanata Dino Melaye dake wakiltar mazabar kudancin jihar Kogi a majalisar dattawan Najeriya ya shiga cikin wani halin tsaka mai wuya saboda yanzu yana fuskantar abubuwa uku: Na daya, jinya da yake fama da ita, ga zargin ‘yan sandan jihar na cewa ya ba wasu ‘yan fashi da makami bindigogi, kana bugu da kari hukumar zabe na shirin kiranyenshi daga majalisar

Yayinda Sanata Dino Melaye daga Jihar Kogi yake jinya a asibiti biyo bayan takaddamar dake tsakaninsa da ‘yan sandan jiharsa, yanzu hukumar zaben Njeriya, INEC ta sanar da kammala shirin kiranyensa daga majalisar dattawan Najeriya.

Hukumar zaben ta ce ranar 28 ga wannan watan zata fara tantance sunayen wadanda zasu kada kuri’ar kiranyenshi ya dawo gida maimakon ya ci gaba da wakiltar mazabar sa, kudancin jihar Kogi.

Alhaji Bagudu Biyombo mai magana da yawun INEC a jihar ya tabbatar zasu tantance sunayen wadanda suka sa hannun a kiranyen. Zasu yi aikin ne daga karfe takwas na safe zuwa biyu na yamma a ranar Asabar mai zuwa bisa doka.

Bayan an tantance sunayen, Alhaji Biyombon yace zasu je mataki na gaba, kodayake bai bayyana matakin ba.

Dangane da cewa shi Sanata Dino Melaye din yana asibiti kwance sanadiyar raunin da ya samu lokacin da aka ce ya dira daga motar ‘yan sanda yayinda take tafiya dashi a ciki zuwa kotu, sai Alhaji Biyombo yace hukumarsu bata da wannan labarin domin bata dashi a rubuce.

Amma wani mai suna Malam Bashir Muhammad mazaunin Lokoja ya zargi gwamnatin jihar Kogin da zama kanwa uwar gami akan wannan yanayin “na gaba kura baya kuma karen daji” da Sanata Dino Melayen ya samu kanshi a ciki. Mutanen kudancin jihar na ganin gwamnatin jihar ce ke yi masa duk kulle-kullen.

Sai dai mataimaki na musamman ga gwamnan jihar akan harkokin kananan hukumomi da masarautu Abdulkarim Abdulmalik wanda shi ma ya fito ne daga kudancin Kogin ya karyata zargin cewa akwai hannun gwamnatin jihar cikin wannan lamari.

Mustapha Nasiru Batsari nada karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG