INEC Na Duba Yiwuwar Zabe Da Na'urar Komfuta a 2023

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, Professor Mahmud Yakubu.

Hukumar zaben Najeriya ta ce gayyaci kamfanoni don kera na'urar da ta dace da nufin komawa kada kuri'a nan gaba ta hanyar na'ura mai kwakwalwa.

Shugaban hukumar zaben farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana cewa hukumar ta gayyaci masu kera na'urorin kada kuri'a daga sassan duniya don gwada yadda za’a yi aiki da fasahar a Najeriya da zai kai ga zabar na'urar da ta fi inganci.

Farfesa Yakubu ya ce, duk kamfanoni 40 da a ka gayyata, za su gwada fasahar su domin tantance ko na'urar zata kara ingancin zabe a Najeriya.

Hukumar zaben ta ce ta bullo da tsarin yanar gizo da a yanzu mutane za su iya ganin sakamakon zaben rumfunan zabe a ranar da a ka kada kuri'a.

Sai dai kawo yanzu ba a tabbatar da dokar da za ta ba hukumar zaben damar aiwatar da wannan tsarin ba.

Rashin sanya hannu da shugaba Buhari bai yi ba kan sabuwar dokar zabe ya jawo suka daga 'yan hamaiya, inda magoya bayan gwamnati ke cewa amincewa da dokar za ta kawo kasadar faduwar jjam'iyar shugaba Buhari don wasu lamura masu sarkakiya.

Saurari rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Zaben Najeriya Ta Gaiyaci Kamfanoni Don Kera Na'urar Kada Kuri'a