Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaushe Za'a Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kogi?


Cibiyar Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kogi
Cibiyar Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kogi

Har yanzu dai jama'ar jihar Kogi suna dakon sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, inda ake jiran sakamakon kananan hukumomi biyu da suka rage.

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta ta jihar Kogi ta bada sanarwar jinkirta bayyana sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jihar har zuwa safiyar yau litinin.

Kawo yanzu dai hukumar zaben ta samu sakamakon zabe daga kananan hukumomi 19 daga cikin 21 da ake dasu a jihar.

A wata matsaya da aka cimma tsakanin hukumar da kuma wakilan jam’iyyun siyasa, babban jami’in hukumar INEC na wucin gadi a zaben na kogi, kuma mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Umar, ya ce hukuma tana jiran sakamakon zabe daga wasu kananan hukumomi gudu biyu da ake fuskantar matsalar zirga zirgan ababen hawa, domin sai anbi ta kan ruwa zuwa jihar Neja kafin a samu shiga ko fitowa daga wadannan lunguna.

Kakakin hukumar zaben ta INEC a jihar Kogi, Alhaji Ahmed Bagudu Biyambo, ya fadawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa da zarar sun samu sakamakon kananan hukumomi biyun da suke jira, idan ya kai su bayyana wanda ya lashe zaben, za su sanar.

Saurari cikakken rahoton wakilinmu Babangida Jibril:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG