Daruruwan 'yan kasar Janhuriyar Nijar dake zaune a Nigeria na ci gaba da yin tururuwa zuwa yin rujistar zabe da hukumar zaben kasar ta Nijar wato SENI ke gudanarwa.
NIger, Nigeria —
Kimanin 'yan kasar Nijar 5000 ne ake sa ran za su yi rijistar zaben da zata basu damar kada kuri'a a Nigeria lokacin gudanar da zaben a can kasar ta Nijar.
Sai dai 'yan Nijar da Muryar Amurka ta tarar suna bin layin rijistar a birnin Minna sun ce lokacin da aka dibar masu ya yi kadan.
A hirar shida Muryar Amurka, babban jami'in hukumar zaben ta kasar Nijar dake aikin rijistar a jihar Neja , Abdu Amadu Ibrahim yace lokacin da aka dibar masu zai ishesu su kammala aikin rijistar.
Bayanai dai sun nuna cewa , idan ba a samu mutane 2000 ba a wannan rijista , 'yan Nijar dake jihar Neja zasu tafi Abuja ne domin kada kuri'a alokacin da za a gudanar da zaben.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5