Hukumar zaben kasar Ghana sun yi watsi da rahotannin kafafen yada labaran cikin gidanta da ke cewa basu shiryawa zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dake tafe ba a ranar 7 ga watan Nuwamba ba.
WASHINGTON DC —
Sun bayyana cewa ‘yan majalisar dokokin kasar na yin wata kwaskwarima ga kudurin zaben da aka maida yin sa zuwa 7 ga Nuwambar a maimakon 7 ga watan Disamba kamar yadda aka saba.
Wasu daga ‘yan majalisar sun nuna damuwarsu kan yiwuwar yin zaben a ranar 7 ga watan Nuwambar, wanda suke ganin ba lallai ne kasar ta iya aiwatar da zaben ba.
Wannan ya biyo bayan ganawar da suka yi da al’ummar mazabunsu da masu ruwa da tsaki.
To amma a wata hira da Muryar Amurka, Eric Dzakpasu, kakakin hukumar zaben ya fadi cewa, hukumarsu na tsara duk mai yiwuwa don ganin an yi zaben kamar yadda aka tsara yinsa.