Amfani da kudade domin sayen kuri’un masu kadawa a ranar zabe, wata dadaddiyar al’ada ce da mafi yawancin ‘yan siyasa a kasashen Afrika ke fakewa da ita domin samun nasara a zabe.
Lura da yadda wannan mummunar dabi’a ke kokarin samun gindin zama a Nijer, hakan ya sa hukumar yaki da cin hanci wato HALCIA ta kudiri aniyar daukar matakai a zabubbukan kasar da ke tafe, inji Madame Amadou Zara Idrissa Massi, kwamishiyar hukumar ta HALCIA.
Bayanai sun yi nuni da cewa masu magudin zabe kan yi amfani da hanyoyi iri-iri don cimma burin da suka sa gaba, inda sau tari sukan hada baki da baragurbin malaman zabe, hakan ya sa hukumar HALCIA ta dauki aniyar toshe wannan kafa.
Ranar yaki da cin hanci da rashawa wani lokaci ne da kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya ke bitar aiyukan da suka gudanar a tsawon watanni 12. A Nijer, alamu na nunin an sami nasarori da dama, ko da yake har yanzu da sauran rina a kaba, a cewar daraktan watsa labaran hukumar HALCIA, Moutari Attaou.
Tsaikon da ake fuskanta wajen hukunta wadanda aka samu da laifin cin hanci ko handamar dukiyar jama’a, da uwa uba jahilci a wajen al’umma, na daga cikin matsalolin da ke dabaibaye aiyukan yaki da cin hanci da rashawa a Nijer.
Wani binciken kungiyar Transparency Intarnational mai yaki da cin hanci da rashawa ya saka Nijer a sahun kasashen da cin hanci ke shafar dukkan fannoni na rayuwa.
Ga rohoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5