Jami'an da Kano zata tura Abuja koyon dabarun yaki da cin hanci da rashawa da duk wata almundahana zasu kwashe makonni takwas suna yi.
Wannan shirin ya biyo bayan wata ganawa ce tsakanin jami'an ICPC da na gwamnatin Kano inda suka yi yarjejeniya akan shirin da kuma yin aiki tare domin cimma nasara..
Kwamred Magaji shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ya yi karin haske. Yace suna gaf da bude ofisoshi a duk kananan hukumomin jihar 44 kuma akwai bukatar ma'aikata da yawa kuma dole su horas da ma'aikatan..Saboda horaswar suka nemi hukumar ICPC ta taimaka tunda tana da kwalaji na musamman akan aiki.
Dalili ke nan da ita ICPC ta je Kano ta ga abubuwan da za'a koyawa jami'an hukumar ta Kano. Bayan ICPC ma hukumar ta Kano zata tuntubi EFCC domin ita ma tana da nata kwalajin no horas da jami'anta.
Ahmed Abdul dake cikin ayarin shugaban kwalajin koyas da dabarun hana rashawa ta Najeriya Farfasa Shola Akinrinade ya kara haske kan yadda horon zai kasance. Zasu horas dasu yadda ake gan cin hanci da rashawa da almundahana da dai saurarnsu kana zasu bada takardar horo ga duk wanda ya kammala karatunsa a kwalajin.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5