Wannan shine karo na ukku da majilisar dokokin jihar kanon ke shirya taron jin raayin jamaa akan kudirin kasafin kudi .
Honarabul Kabir Alhasan Rim dake zaman kakakin majilisar ya bayyana dalilin makasudin shirya irin wannan taron.
‘’Daya daga cikin ka’idojin da muka shinfida wa kanmu akan wani lamari da ya taso ko zai taso wandaya shafi al’ummarmu yana da kyau a sanar dasu kuma a kira su, su bada shawara kuma su bada gudun mowa da basirar su da ALLAH ya basu kuma su haska muna mu abinda mu ba zamu iya hangowa ba koma ita gwamnati abinda bata hango ba’’
Mallam Sani Shugaban kungiyar nakasassu na kasa reshen jihar Kano ya koka ne akan rashin kulawa da gwamnati ta baiwa shaanin rayuwar su cikin kasafin. Ga kuma abinda yake cewa.
‘’Cikin nakasassun akwai wadanda nakasar bata hana su suyi sana’a ba, wadannan sai a tallafa musu da jarin da zasu yi sanaar su rike kansu, akwai kuma wadanda tsufa ba zata barsu suyi sanaar ba ko ance suyi, su kuma wadandan ya cancanci a basu abinda zasu rika ci gaba da tafiyar da rayuwar su, amma sai kaga shugabannin kananan hukumomi sun aba yan siyasa ‘yan uwan su ko kuma su juya sui ta wata hark aba ita akeyi ba don haka muke son ayi wa abin tsari ayi wa abin doka’’.
Shi kuwa Murtala Dan kanawa dake zaman shugaban kungiyar habbaka mazauna karkara a kano cewa yayi .
Ganin irin manyan kudin da aka sa a kiwon lafiya munyi goodiya mun san akwai hikima cikin wannan al’amari to amma babban abinda aka manta duk wannan abinda aka sa cikin kiwon lafiya kawai an tare ne ayi a Murtala ayi a cikin kano idan aka samu akace ana da asibiti a cikin ko wace karamar hukuma mai likita tabbatacce da yake zaune wannan zaisa a rage wa asibitin murtala nauyi, wannan kasafin kudi ne na dogaro da kai’’
Ga Mumud Ibrahim Kwari da Karin bayani