A daidai lokacin da Najeriya ke shirin yin zaben shekara ta 2023, Hukumar Wayar da Kan Al'umma ta yi yunkurin hada kan mata domin su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kan kasar ganin cewa su ne iyaye wadanda suke da sigar kyawawan halaye.
Dokta Garba Abari, shugaban Hukumar Wayar da Kan Al'umma ta kasa, ya jaddada dalilan kafa wanan Kungiyar inda ya ce Najeriya ta fahimci muhimmancin wanzar da zaman lafiya da samar da zaman lafiya wajen yin amfani da mata da kuma kokarin riga kafin rikice rikice da kan shafi mata da yara. Abari ya ce ba wa mata dama ta gudanar da hidindimun su zai kawo wa kasa daidaito a al'amuranta, musamman ma a wanan lokaci da kasar ke bukatar hadin kai da kaunar juna.
Shugabar Kungiyar NAWA ta kasa Hajiya Hauwa Hayatu Bagu ta ce za ta jagoranci tattaki na mata miliyan biyar domin su nuna cewa zama lafiya ya fi zama dan sarki.
Hauwa ta ce lokaci ya yi da mutanen kasar za su farga su daina amincewa da rarrabuwar kawuna ta addini da bangaranci domin sai ana zaune lafiya ne za iya gina kasa.
Babban Sakataren Kungiyar Ambasada Ibrahim Waiyya ya ce ya amince da mukamin da aka bashi ne saboda an dade ana yi wa mata wayo a Najeriya, saboda haka zai taimaka wajen karfafa mata domin su nemi hakkokinsu musamman daga wadanda ke takarar mukamai a Najeriya.
Waiyya ya ce ba zai yarda a cuci mata ba a wannan karon, Komi sai an shiga yarjejeniya. Waiyya ya ce yana nan tare da su ba gudu ba ja da baya.
Daya daga cikin Jagororin Kungiyar wacce ita ce za ta jagoranci NAWA ta Jihar Kaduna, Amina Shuaibu Kazaure, ta ce ta san cewa Jihar Kaduna ta dade da samun rarrabuwar Kawuna, amma za ta yi aiki tukuru wajen ganin an dawo da soyayya da rikon amana da aka san Kaduna da shi. Amina ta ce za ta rungumi kowa da kowa ba tare da wani banbancin addini ko kabila ba.
An rarraba wa mata Satifiket na shaidar zama jagororin Kungiyar a Jihohi 36 na kasar da Birnin Tarayya Abuja.
Ga rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5