Hukumar USAID Ta Kaddamar Da Wani Sabon Shirin Ilimi A Jihar Bauchi

USAID

Hukumar USAID ta kasar Amurka ta kaddamar da shirin bunkasa ilmi na tsawon shekaru biyar a jihar Bauchi, domin tallafawa wajen ganin kowanne yaro ya sami ilimi a jihar.

Darektan hukumar ta USAID a Najeriya Mr. Micheal Harvey, shine ya jagoranci kaddamar da shirin da aka gudanar a Otel din ZAranda dake garin bauchi. Shirin dai zai fi maida hankali ne ga ilmin almajirai dana yan mata dakuma matan aure.

Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abubakar, yace shirin na da matukar muhimmanci domin akwai kudi kimanin Dalar Amurka Miliyan 15 da aka bayar za ayi amfani da su a jihohi 3 na Arewacin Najeriya.

Hajiya Yalwa Abubakar Tafawa Balewa, itace babbar sakatariya a hukumar yaki da jahilci, wadda ta nuna jin dadin ta ga wannan taimako da kasar Amurka tayi na ganin an koyar da yara almajirai da yan mata.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar USAID Ta Kaddamar Da Wani Sabon Shirin Ilimi A Jihar Bauchi - 2'25"