Hukumar UNHCR Da Gwamnatin Ghana Na Daukar Matakan Inganta Rayuwar 'Yan Gudun Hijira a Ghana

Hukumar UNHCR a Ghana

Daga Sapeliga a gundumar Bawku ta yamma a jihar maso gabashin kasar Ghana, daruruwan ‘yan gudun hijira daga Burkina Faso na ci gaba da neman mafaka a Ghana.

Madi Zabre, na daya daga cikin ‘yan gudun Hijirar, ya fada wa manema labarai cewa rikicin ta'addanci ne ya yi sanadin tserewarsu daga Burkina zuwa Ghana.

“A nan muna cikin kwanciyar hankali, matsalar mu dai ita ce bamu da isasshen abinci da ruwan sha, ‘ya'yanmu basu zuwa makaranta kuma babu cibiyar kula da marasa lafiya mai inganci, a saboda haka muna bukatar taimako."

Ita kuwa Zabre Zainabu, cewa ta yi mata daga cikinsu na fama da matsalar rashin audugar al'ada kuma su da ‘ya'yansu basu da kayan sawa.

Yan bindiga a jihar Sokoto

Hare-haren ta'addanci a kasar Burkina Faso mai makwabtaka da Ghana ne suka sa al’umar kasar da yawansu ya zarta 4,000 guduwa zuwa wasu yankunan kasar Ghana a kusa da iyakar Burkina Faso, yankunan da suka hada da Pusuogu, Kubugu, Sapeliga, Widnaba, da sauransu.

Hukumar kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UNHCR ta bayyana damuwa game da matsalar, a cewar Esther Kiagu, wakiliyar hukumar a Ghana a lokacin da ta ziyarci sansanin ‘yan gudun hijirar.

"Idan kuka kalli wannan matsugunnin da ‘yan gudun hijira ke samun mafaka zaku ga cewa babu wajen barci mai walwala. Abin damuwa shi ne wannan matsugunnin na dab da iyakar Burkina Faso kuma wannan na barazana ga tsaronsu," a cewar Kiagu.

Hukumar UNHCR a Ghana

Sai dai ba bakin haure ne kadai rayuwarsu ke tattare da hadari ba, har ma da wasu al’umar Ghana saboda ana iya samun miyagun mutane da zasu yi amfani da wannan damar ta kasancewar bakin haure su aikata ba daidai ba.

Umar Sanda Ahmad, mai sharhi kan harkar tsaron ciki da wajen Ghana, ya bukaci hukumomi a Ghana su ringa tantance bakin haure kafin basu damar shiga kasar.

Duk da kokarin da hukumar kula da bakin haure a Ghana ke yi wajen taimakon bakin hauren, wasu ‘yan Burkina Faso da ke zama Ghana suna tattara kayan abinci domin tallafa wa bakin hauren.

Hukumar UNHCR a Ghana

Bayan da wasu mazauna jihar Ashanti suka taimaka da kayan abinci, Ziekan Diani, shugabar kwamitin da ke da alhakin tattara kayan agaji a Ghana, ta fada wa manema labarai cewa sun samu buhunan masara daga gundumar Ejura kuma abincin zai taimaka wa ‘yan gudun hijira su ciyar da kansu da ‘ya'yansu.

Matsalar tsaro a Burkina Faso da Mali dai na ci gaba da haifar da barazana a yankin yammacin Afrika, abin da masharhanta ke cewa ya kamata a dauki mataki. Sai dai tuni gwamnatin Amurka ya yi shelar zuba kimanin dala miliyan dari domin karfafa tsaro a yankin.

Saurari cikakken rahoton Hamza Adam:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar UNHCR Da Gwamnatin Ghana Na Daukar Matakan Inganta Rayuwar 'Yan Gudun Hijira a Ghana