Hukumar dake kula da wasan kwallon Kafa ta nahiyar turai Uefa ta na tuhumar kungiyar kwallon Kafa ta Atletico Madrid ta kasar Spain, bisa zarginta da nuna wariyar launin fata a wasan da suka buga na karshe na cin kofin Europe League na shekarar 2017/18 a ranar talata 16/5/2018 tsakanita da Olympicos Marseille inda ta samu nasarar lashe gasar bayan ta doke Marseille da kwallaye 3-0.
Uefa ta ce magoya bayan Atletico Madrid, sun daga kyalle mai dauke da rubutun da yake nuna wariyar launi haka kuma sun yi kunna wuta tare da jefa wasu abubuwa cikin fili yayin wasan wanda yin haka ya saba wa dokokin hukumar.
Don haka hukumar ta ce kwamintin ladaftarwa na Uefa zai yi zama akan wannan alamarin ranar 31 ga watan Mayu 2018 domin daukar mataki game da lamarin.
Your browser doesn’t support HTML5