Hukumar Tsaro Ta Kama Wani Mutum Mai Sayar Da 'Ya'Yansa

Ayuba John da dansa mai shekaru 3 da yake niyyar sayarwa

Hukumar tsaro da bada kariya ga al'umma reshen jihar Nasarawa tayi nasarar cafke wani mutum mai shekaru 42 da laifin sayar da dansa.

Kwamandan rundunar Civil Defence na jihar Nasarawa, Muhammad Gidado Fari, yace jami’ansu sun yi amfani da kwarewar aikinsu wajen damke mutumin da yayi niyyar sayar da dansa mai shekaru 3, kan kudi naira miliyan 5.

Kwamandan yace mutumin mai mata 5, da kuma yara 23, an kama shi karo na biyu, domin ya taba sayar da 'yar shi, wadda ake zato anyi tsafi da ita a jihar Owerri.

Ko da aka tambayi wanda ake zargin, mai suna Ayuba John, sai yace yaso ya sayar da yaron mai suna Solomon ne don ya sami abin rufin asiri.

A wani rahoto kuma, rundunar ta Civil Defence ta kama wani mutum wanda ke lalata da 'yarsa mai shekara 10, Inda mahaifiyar yarinyar ta kamashi da 'yar.

Ga rahoto cikin sauti da Zainab Babaji ta hada muna.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Tsaro Ta Kama Wani Mutum Mai Sayar Da 'Yayansa