Hukumar Zaben Kamaru Tayi Taronta Na Farko

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya

Tun lokacin da aka kafata sai yanzu hukumar zaben Kamaru ta samu sukunin yin taron farko inda ta soma shirye-shiryen gudanar da zaben kasar na shekarar 2018.

Jami'an hukumar sun yi taron tsawon kwanaki uku a zauren shawara na kasa dake birnin Yaounde

Manufar taron shi ne tantance sunayen wadanda suka kai su jefa kuri'a kasancewa akwai wasu matasa da yanzu shekarunsu sun kai su kada kuri'a kamar yadda kundun zaben kasar ya kayyade. Hukumar ta mayar da hankali musamman akan mata da nakasassu.

Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta Abdullahi Babale yace dole ne su tsaya tsayin daka domin ganin cewa kowane dan kasa ya samu katin zabensa.

Babale yace tun farkon shekarar nan zuwa yanzu sun rubuta sunayen mutane kimanin miliyan shida da dubu dari tara kuma duk sun samu katin kada zabe da zasu yi anfani dasu a zabe mai zuwa.

Yace hukumar tana da ka'idodinta da kuma dokokinta. Na farko hukumar zata ba kowa 'yancinsa walau mace ko namiji. Kowane dan kasa kuma dole ne ya je mazabarsa kafin ya kada kuri'a. Hukumar zata ba kowa damar zaben abun da yake so a zuciyarsa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Zaben Kamaru Tayi Taronta Na Farko - 2' 05"