Hukumar Tabbatar Da Da'ar Ma'aikata A Najeriya Ta Gayyaci Ministan Cikin Gida

Ministan Cikin Gidan Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo

Wasu kafofin yada labaran Najeriya sun ruwaito cewa, Hukumar Tabbatar da Da’a a Najeriya wato Code of Conduct Bureau, ko kuma CCB a takaice ta gayyaci Ministan Ma’aikatar Cikin Gida ta Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ofishinta don amsa tamabayoyi da aka alakanta da badakalar da aka gano a Ma’aikatar Jinkai da Walwalar Al'umma wanda ake zargin kamfanin ministan ya ci gajiyar kwangilar bogi na naira miliyan 438.

Wata takadar da ta fito daga ofishin hukumar da’ar a yau Litinin ya bayyana cewa hukumar ta aikewa ministan da ke fuskantar tuhumar, takardar gayyata don neman ya bayyana gaban ta a gobe, Talata 16 ga watan Janairun 2024, a shalkwatar ofishin hukumar da ke ginin ofisoshin gwamnatin tarayya da ke babban birnin Abuja.

Takardar wanda ke dauke da sa hannun Darektan Bincike na Hukumar Da’ar, Gwimi S.P a madadin Shugaban Hukumar Murtala Aliyu, ya yi nuni da cewa, hukumar ta gayyaci ministan ne bisa ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yiwa gyaran fuska a 1999 shimfida ta 3 kashi daya uku cikin baka (e) ta baiwa hukumar.

Bayanan da wasikar da hukumar ta aikewa ministan ta ce, “hukumar ta na gudanar da bincike a kan take ka’idojin da hukumar da’ar Najeriya ta shimfida wa jami’an gwamnati don tabbatar da da’a inda sunan ka ya bayyana a fili.

"A dalilin haka ne ya sa muke gayyatar ka ka zo shalkwatar ofishin mu gobe talata 16 ga watan Janairu da misalin karfe 11:00 na safe".

Tunji-Ojo ya shiga wannan rudun ne bayan da ya bayyana cewa wani kamfani da ke mallakin ministan, mai suna new Planet Projects na daga cikin jerin kamfanoni da suka ci gajiyar badakalar kudin da ta auku a Ma’aikatar Jinkai da Walwalar Al’umma wanda ya kai ga Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da ministan ma’aikatar, Betta Edu.

Ko da yake, Tunji-Ojo ya fito ya bayyana cewa tuni ya janye daga mukaminshi na darekta a kamfanin da ya kafa tare da mai dakinsa, amma kuma ta ci gaba da rike kaso mafi girma a kamfanin.