Cire shugaban kwamitin kasafin kudi Abdulmummuni Jibrin ya kaiga tona asirin yadda wai aka yi aringizo a lokacin da majalisar ke duba kasafin kudin da shugaban kasa ya gabatar mata.
Kwabewar da aka yi masa ya jawo cece kuce da caccakar juna tsakanin Abdulmummuni Jibrin da magoya bayansa da bangaren kakakin majalisar inda kowane bangare ke zargin juna da yin aringizon.
Wannan lamarin ya sa hukumar SSS ta rufe ofishin kasafin kudi na majalisar saboda gudun kada wasu muhimman takardu su bace da zara 'yan majalisar sun dawo daga hutu.
To saidai mataimakiyar mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye Binta Bello ta PDP Gombe ta kalubali batun aringizon inda tace shugaban kwamitin ksafin kudi shi ne bai yi masu aiki ba.Wai kudin da aka kara rabawa za'a yi tsakanin majalisarsu da ta dattawa.
Lokacin da suke aiki akan kasafin sun kira gefen zartaswa su zo su gyara tare kuma a lokacin da suka gama aiki babu wanda ya yi korafi.Ta hakikance maganar aringizo ba gaskiya ba ce saboda tun lokacin Obasajo ake sawa 'yan majalisun biyu nera biliyan dari. Ba yau aka fara ba.
Amma 'yan kungiyar sa ido a harkokin majalisa, shugaban kungiyar Awal Musa Rafsanjani yace dole ne a yi bincike. Babu wanda zai yadda a cigaba da kwasan makudan kudi ana ragargazawa. Yace babu wata kasa a duniya da ake irin wannan almundahana kamar Najeriya. Dole a yi bincike a dakatar da sace-sace da ake yi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5