Hukumar Shirya Wasannin Kwallon Kafa Ta Najeriya Ta Rufe Wasu Filayen Wasa

Kamfanin dake shirya wasannin lig na Firimiya a tarayyar Najeriya LMC ya dakaratar da buga wasannin a wasu filayen wasa guda hudu sakamakon rashin kyauwun filin Na tsawon makwanni biyu.

Filayen da lamarin ya Shafa sune Dan Anyiam dake Owerri, inda kungiyar Heathland suke na kungiyar Niger Tornadoes dake jihar Niger, sai filin wasa na August 27 dake Damaturu inda Yobe Stars suke fafata wasannin su da kuma Umuahia Township Stadium na Abia Warriors.

Hukumar LMC ta ce ba za'a sake wani wasa a filayen ba har sai an gyara kuma Kwamintin masu binceke ya tabbatar da ingancin filayen kafin nan.

Haka kuma ya umurci dukkan kulob din da lamarin ya Shafa su zabi duk inda suka ga ya dace su yi wasa amman banda wadannan filayen da aka dakartar.

A wani Labarin kuwa dan wasan baya na kungiyar Kano Pillars a tarayyar Najeriya Chinedu Udoji, ya rasu a jiya da daddare sakamakon hatsarin Mota da yayi a hanyarsa ta dawo gida bayan ya kai ziyara ga takwarorinsa na tsohon kulob dinsa Enyimba wadda a jiya sukayi wasa da Kano Pillars a wasan Firimiya lig mako na tara inda aka tashi 1-1

Udoji ya gamu da ajalinsane a kan titin Independent na Bompai dake Jihar Kano ta bakin jami'in watsa labarai na Kano Pillars Malikawa ya ce hukumar gudanarwa ta kano Pillars ta bayyana mutuwar a matsayin Babbab rashi ga kungiyar kawai ba harda kasa baki daya.

haka kuma ya bayyana dan wasan dacewar mutum ne mai hankali wadda ya sadaukar da kansa a kan abinda ya kware, Jami'an kulob din suna sarrafa dukkan takardun da suka dace kafin su dauki gawar mamacin zuwa ga iyalinsa don birnewa.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Shirya Wasannin Kwallon Kafa Ta Najeriya Ta Rufe Wasu Filayen Wasa