Hukumar kula da Jami'o'in Najeriya NUC, ta ce, karyar zama Farfesa babban laifi ne saboda haka za a iya jefa duk Farfesa na bogi da a ka samu da wannan laifin gidan yari.
Daraktan labarun hukumar Ibrahim Usman Yakasai, ya bayyana haka ne da yake karin haske kan bankado Farfesoshi 100 na karya da hukumar ta yi.
Yakasai ya ce, masu da'awar Farfesoshin ba su kai samun matsayin ba, amma su na amfani da sunan don burga a tsakanin jama'a.
Memba na kwamitin kafa Jami'ar Assalam ta JIBWIS a Hadeja, Farfesa Aliyu Bunza na jami'ar Danfodio ya ce, ko mutum ya kai Farfesa ba zai cika shehun malami nan take ba.
NUC na wallafa littafi duk shekaru da ke kunshe da jerin sunayen farfesoshin inda yanzu akwai kimanin farfesoshi dubu 10 a Najeriya.
Hukumar ta ce ba a yarda malamin jami'a ya rika koyarwa a fiye da jami'a biyu ba, kuma ya zama wajibi ya yi aiki na tsawon sa'a 18 a mako.
Saurari rohoton wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya, cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5