Kasa da sa’o’i 24 da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasan Najeriya wato NRC za ta fara aikin jigilar fasinjoji gadan-gaban tsakanin Abuja zuwa Kaduna, bayan kwashe sama da watanni 7 da dakatar da aiki sakamakon harin da 'yan ta’adda suka kai kan daya daga cikin jiragen kasan Najeriya a watan Maris, Ma’aikatar Sufuri da Hukumar NRC sun yi jigilar 'yan jarida da ma’aikatansu daga Abuja zuwa Kaduna don gwaji da duba matakan tsaro da gwamnati ta dauka a kan hanyar don dakile wani hari da kare rayuka da dukiyoyin fasinjoji da za a fara jigila daga ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba.
Ma’aikatar sufuri tare da hadin gwiwar hukumar NRC din sun gudanar da wannan aikin gwajin ne a yau Lahadi, 27 ga watan Nuwamban shekarar 2022 inda suka sami gomman 'yan jarida da ma’aikata cikin jirgin da ya yi tafiya tsakanin Abuja zuwa Kaduna da zummar duba matakan tsaron da gwamnatin kasar ta dauka.
Dalilin gudanar da aikin dai ba ya rasa nasaba da gwajin lafiyar jirgin da duba matakan tsaron da aka sanya don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya da zasu koma zirga-zirga kan hanyar layin dogon.
Mu’azu Jaji Sambo shi ne ministan sufuri a Najeriya. Ya yi karin haske, kamar yadda za a ji.
A wani Bangare kuma, shugaban sashen hulda da jama’ar hukumar NRC, Yakub Mahmud, ya ce aikin da aka gudanar a yau ya nuna cewa a shirye gwamnatin Najeriya ta ke ta inganta tsaro a dukannin matakai.
Ko mene ne ma’aikata da yan jarida da suka kasance a cikin tawagar da su ka yi tafiya tsakanin Abuja ke cewa a kań matakin yin gwajin aikin jirgin kasar. Ga karin bayani, kamar yadda za a ji a cikakken rahoton idan an latsa madangwalin sauti.
A yanzu dai masu bibiyar al’ammura sun ce za su zura ido su ga yadda al’amura za su kasance a sha’anin zirga-zirgar fasinjojin jirgin kasa tsakakanin Abuja zuwa Kaduna din.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdurra'uf:
Your browser doesn’t support HTML5