Hukumar ta ce karin ko kadan bai kai yanda a ke yayatawa ba, amma an yi shi bi sa yanayin tattalin arziki da darajar Naira.
Hukumar kula da farashin lantarkin NERC ta ce karin da ma bai fi kashi 2% ya bambanta tsakanin kamfanonin dillancin wutar 11 a fadin Najeriya.
Jami'in labarun hukumar Micheal Folaseyi, ya ce farashin ya danganta ga biyan ma'aunin wuta a sa'a daya daga Naira biyu zuwa Naira hudu.
Folaseyi ya ce hakika an yi kari da ya shafi wadanda a baya bai shafi masu shan wutar na tsawon sa'a 12 a wuni.
Azuzuwan masu samun wuta guda biyar daga masu samu a duk wuni zuwa ajin karshe na masu amfana na tsawon sa'a hudu kacal.
Tun a bara ministan wutar lantarki injiniya Saleh Mamman, ya ce dillalan wutar ba su da jarin sayan wadatacciyar wutar da za ta wadaci jama'a.
Tuni 'yan Najeriya sun fara nuna bacin rai ga yanda a ke samun kwan gaba kwan baya a farashin wutar.
Wani dan jarida mai amfani da wutar a arewa maso gabar Yusuf Ishaq Baji, na cewa karin ya shafi har inda a baya ba a biya, kamar wuraren ibada.
A zamanin mulkin shugaba Buhari daga 2015 zuwa bana, an kara kudin wutar kimanin sau biyar. Mutane za su fi fahimtar karin ta yawan kudin da su ke biya ko saurin karewar katin kudin wutar.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5