A farkon makon nan ne wani mummunan rikici ya faru tsakanin Fulani makiyaya da ‘yan kabilar Bachama dake yankin Numan ad Demsa a jihar Adamawa. Baya ga hasarar rayukan da aka samu, rikicin ya kuma tilastawa wasu yin gudun hijira zuwa wasu kauyukan da ke makwabtaka da su da kuma jihar Gombe.
Hukumar bada agajin jinkai ta Najeriya da ake kira NEMA a takaice, ta kaiwa wadanda harin ya shafa taimakon agajin jinkai.
A wata hira da sashin Hausa ta wayar tarho, shugaban hukumar ta NEMA mai kula da harkokin hukumar a yankin arewa maso Najeriya, Bashir Idris Garga ya tabbatar da matakin taimakon da hukumar ta dauka. A cewar Bashir, mutane kimanin 1,500 ke gudun hijira a wata makaranta dake garin Cham, wasu kuma suna garin Kumo kuma hukumar ta tura wakilanta zuwa wadannan garuruwan.
Sai dai shugaban hukumar ya ce har yanzu ba a iya tantance adadin wadanda rikicin ya shafa ba, ko suka rasa rayukansu saboda dalilan tsaro. Amma yace idan jami’an tsaro suka gama bincikensu, suka basu kariyar shiga wurin zasu ga abinda zasu yiwa wadanda basu gudu.
Your browser doesn’t support HTML5