Jam’iyar PDP a jihar Taraba ta zargi gwamnatin APC a Najeriya da neman ruguza tattalin arzikin Najeriya batun da ta ce shi ya jefa yan kasar cikin halin ni yasu. PDP din ta yi sukan ne yayin wani gangami na karbar wasu yan APC da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP,batun da ke cigaba da jawo musayar kalamai a jihar.
Yayin da PDP ke murnar, itama dai APC ta yi nata wawan kamu na tsohon mukaddashin gwamnan jihar da dinbin magoya bayansa da suka bar PDP zuwa APC.
Da yake jawabi Shugaban jam’iyar PDP na jihar Taraba Victor Bala Kona yayin wani gangamin sauya shekar yan jam’iyar APC zuwa PDP a Taraba ya ce APC yaudara ta kawo.
Shima a jawabinsa gwamnan jihar Darius Dickson Isiyaku wanda mataimakinsa Haruna Manu ya wakilce shi ya ce burin gwamnatinsu shine adalci ga kowa.
Tun farko wasu yayan jam’iyar APC da suka sauya shekar sun danganta rashin adalci da rikicin cikin gida da ya dabaibayi jam’iyar a jihar da cewa su suka sasu ficewa.
To sai dai kuma yayin da PDP ke murna, ita ma jam’iyYar APC a jihar ta yi wawan kamu, inda tsohon mukaddashin gwamnan jihar Garba Umar (UTC) da shi da dinbin magoya bayansa da ma wadanda suka rike mukamai a zamaninsa suka sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Tun komowar demokaradiyya jam’iyar PDP ce ke mulki a jihar Taraba,ko da yake a zaben shekarar 2015 da jibin goshi jam’iyYar ta kwaci kanta daga APC, kuma yanzu an zura ido a ga yadda wannan sabuwar kasuwar sauya shekan zata kaya.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum