Kwamandan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a shiyar Adamawa Mr. Yakubu Kibo, ya nunawa manema labarai wasu muggan kwayoyi, da kuma tabar wiwi, da kudinsu ya kai Naira miliyan 15, da kuma dillalan kwayoyin da aka cafke.
Baya ga dillalan kwayoyin hakanan kuma jami'an hukumar ta NDLEA, sun cafke wani dan garkuwa da jama'a, domin neman kudin fansa.
Ganin yadda matsalar sha da fataucin muggan kwayoyi ke kara ta'azzara, yasa hukumar NDLEA hada guiwa da wasu kungiyoyin sa kai irinsu Alliance For Youth Awareness wato AFYA.
Ko a 'yan watannin nan akwai 'yan Najeriya da dama da aka cafke, ko yankewa haddi a wasu kasashen waje kan laifin fataucin miyagun kwayoyi, lamarin da masana ke cewa dole a tashi tsaye.
A saurari cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5