Amma kwararru a fanin zamantakewan dan Adam na cewa dole a hukunta wadanda suka yi laifi a harkar gudanar da tsarin baki daya.
Wannan mataki yana zuwa ne jim kadan bayan da Ministar Kula da Ma'aikatar Jinkai da Rage Radaddin Talauci, Betta Edu ta dakatar da shirn N-Power domin a yi bincike yawancin wadanda aka dauka aikin kula da biyan masu cin gajiyar tallafin N-Power wadanda aka fi sani da consultants.
Kafin a kai ga dakatar da shirin, mai magana da yawun hukumar N-Power Jamaludeen Kabir ya ce Kungiyar Batch 'C' ta rubuta wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu takarda cewa ba a biya su alawus din su na wattani 9 ba.
Jamaludeen ya kara da cewa binciken da Ma'akatar Jinkai ta baiyanar da inda wadannan kudade suke kuma ba da jimawa ba za a fara biyan wadanda suka ci gajiyar shirin kudaden su na wattani 9. Jamaludeen ya ce ba a riga an kammala bincike kan consultants din ba, amma an gano wadanda suka yi horo don inganta rayuwar su, kuma su ne za a biya su bashin da suke bin wannan ma'aikata.
To sai dai ga kwararre a fanin zamantakewan dan Adam kuma malami a Jami'ar Abuja, Dokta Abu Hamisu yana ganin akwai abin dubawa a wannan tsarin.
Abu ya ce kamata yayi a bi diddigi na wadanda suka yi kuskure wajen aiwatar da aikin a hukunta su, domin haka ake samun cigaba a irin wannan yanayi. Abu ya ce duk kasashen da suka cigaba sai sun bi tsari sosai sannan ake samun nasara. Ya kuma ce inza a bi shawarar sa, a bar wannan tsarin yadda ya ke amma a tabbatar da an sa ido sosai domin cire baragurbi wadanda ba sa son cigaban tsarin, kuma a hukunta su domin ya zama izina ga wasu.
Yaya, daya cikin wadanda suka ci gajiyar shirin N-Power, Mohammed Aliyu ya ji da wannan labari da ke cewa za a biya su kudaden da suke bin Ma'aikatar bashi har na wattani 9, sai ya ce, a hakikanin gaskiya yau yana cike da farin ciki, na jin wannan labari da dumidumin sa cewa za a biya su kudaden su. Aliyu ya ce yana jinjina ga Gwamnatin Tarraiya da ita Ministar Ma'aikatar Jinkai da Rage RadaddinTalauci.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5