Hukumar Man Fetur Ta Kasa Ta Dauki Dawainiyar Karatun Hazikin Dalibi

Al-amin Bashir Bugaje

Hukumar harkokin man Fetur ta Najeriya, ta bada sanarwar daukar dawainiyar karatun wani dalibi daya fi sauran dalibai samun sakamon kammala karatu mai kyau a zangon kammala karatu na shekarar 2016/17 a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, har zuwa matakin digirin digir-gir.

Manajan Drakatan kungiyar, Dr MaiKanti Baru, wanda ya bada sanarwar a yayin da yake jawabi a bikin yaye dalibai da aka gudanar a Zaria, ranar asabar data gabata. Ya bayyana cewa hukumar zata dauki nauyin karatun dalibin mai suna Al-amin Bashir Bugaje, har zuwa matakin karatu na digirin digir-gir a kowace jami’a yake so a duniya.

A bikin yaye daliban na wannan shekarar, dalibin mai shekaru 23 da haihuwa ya kammala karatun sa ne da sakamakon aji na farko wato First Class a turance da maki (CGPA 4.93) a fannin harkokin wutar laturoni, kokuma Electrical Engineering a turance, wanda ya kasance dalibin da yafi dukkan daliban da suka kammala karatu a wannan shekarar fita da maki mai yawa.