Rukunin gidajen shi ne na farko da Majalisar Dinkin Duniya ta samar zai kasance matsuguni na din-din-din ga wadanda bala'i ko wani tashin hankali ya shafa har lokacin da zasu samu natsuwar komawa wajajensu na asali.
Yayinda take kaddamar da gidajen wakiliyar UNHCR ta MDD a Najeriya da kasashen Afirka ta Yamma Anje Dikonje Atangana tace kasancewar kasar Benue ta sha fama da rikicin cikin gida da matsaloli tsakanin makiyaya da manoma ya sa mutane fiye da dubu dari uku gujewa daga muhallansu.
Inji Atangana babban abun da 'yan gudun hijiran ke bukata musamman mata da yara shi ne tsaro da samun rufi a kansu. Tace da damansu suna bukatan abinci da sana'o'i da zasu inganta rayuwarsu. Dalilin da ya sa hukumar ta kai wasu daga cikin mutanen kasar Benin domin koyon aikin noma da kiwon kifi da dabbobi irin na zamani.
Mataimakin gwamnan jihar Benue wanda ya karbi jidajen a madadin gwamnatin jihar yace kananan hukumomi 12 ne daga cikin kananan hukumomi 23 dake jihar suka fuskanci munanan ayyukan ta'adanci lamarin da ya sa dubban jama'a ke gudun hijira a ciki da wajen jihar.
Mataimakin gwamnan yace idan akwai hadin kai tsakanin gwamnati da hukumomi irin na Majalisar Dinkin Duniya za'a samu cigaba tare da inganta rayuwar mutane.
Wadanda suka samu gidajen sun gode suna cewa yanzu sun samu matsuguni, su da 'ya'yansu.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5