Hukumar sa ido mai suna IMB tace yaduwar ciwon shan inna a Najeriya da Pakistan yana barazana ga nasarar shawo kan cutar a kasashen duniya.
Hukumar wadda aka kafa karkashin shirin yaki da ciwon shan inna na duniya “Global Polio Eradication Initiave (GPEI) ta bayyana damuwa dangane da karuwar yaduwar cutar shan inna a Najeriya da kuma Pakistan da cewa, kasashen biyu suna barazana matuka ga sanarar shawo kan cutar a duniya baki daya.
Cibiyar GPEI wata cibiya ce dake gudanar da wani shirin hadin guiwa da ta kunshi hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatocin kasashen ke aiwatarwa, karkashin jagorancin Hukumar lafiya ta duniya, da kulob din Rotary International, da cibiyar yaki ta cututuka ta Amurka (CDC) da kuma Asusun tallafawa kananan yara UNICEF, da nufin kawar da ciwon shan inna a duniya baki daya.
A cikin rahoton hukumar sa ido ta IMP da aka fitar makon jiya an yabawa gwamnatin kasar Indiya sabili da shawo kan cutar inda ba a sami ko mutun daya dauke da cutar ba a kasar tun daga watan Janairu shekara ta 2011, abinda yasa ake dab da aiwatar da ita a matsayin kasar da ta shawo kan ciwon shan inna. Rahoton ya bayyana cewa, “Hukumar sa ido ta damu matuka da karuwar yaduwar ciwon shan inna a Najeriya da Pakistan, yanzu kasashen biyu sun zama da hadarin gaske ga yiwuwar shawo kan cutar a duniya baki daya.”.
Hukumar ta bayyana cewa, nasarar da aka samu a kasar Indiya ya nuna cewa, abu ne mai yiwuwa a iya shawo kan cutar, ta kuma jadada cewa, lallai ne a himmatu domin ganin an shawo kan cutar baki daya, idan ba haka ba kuwa, tayi gargadi da cewa, cutar zata kara bazuwa ta gurgunta dubban kananan yara.
Dangane da Najeriya, cibiyar GPEI tace, an kara samun wadansu kananan yara biyu dauke da cutar makonni biyu da suka shige a jihohin Sakkwato da Zamfara, abinda ya kai adadin kananan yaran da aka samu da cutar zuwa 60 a shekara ta 2011, yayinda aka sami wani karamin yaro daya ranar 14 ga watan Janairu bana dauke da cutar a jihar Borno wanda ya nuna alamun nakasa.
Hukumar sa ido kan ci gaban da ake samu a yaki da cutar shan inna ta kasa da kasa ta fitar da rahoton ne yayinda ake shirin gudanar da wani rukunin shirin yaki da ciwon shan inna a Najeriya inda ma’aikatan jinya ke shiga gida gida suna ba kananan yara rigakafin cutar.