Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar a jiya Litinin cewa ta amince da nau'i biyu na rikafin Korona bairos na AstraZeneca don amfanin gaggawa, matakin da zai bunkasa alluran a duniya cikin makonni masu zuwa.
Kamfanin AstraZeneca-SKBio da ke Koriya ta Kudu da kuma cibiyar Serum ta India ne suka samar da alluran, wadanda WHO ta ce suna da kyau ga duk mutanen da suka wuce shekaru 18.
Kungiyar lafiya ta duniya ta kwashe ‘kasa da wata daya kafin ta tantance bayanai kan inganci da amincin magungunan kafin ta ba da izinin amfanin gaggawa da shi.
Kungiyar Lafiya ta Duniya yanzu za ta rarraba allurai ta hanyar amfani da tsarin COVAX ke samarwa zuwa kasashe masu matsakaici da masu karamin karfi. Amincewar ta kuma bai wa kasashe damar hanzarta yin dokokin cikin gida don shigowa da gudanar da alluran.