Hukumar Kwastan Tayi Wani Wawan Kamu Kusan Bilyan 3.

Irin kayan da hukumar kwastan ta kama

Kwanturolan hukumar kwastan mai kula da shiya ta daya ya yi hira da manema labarai inda ya bayyana nasarorin da suka samu kan 'yan sumoga.

Kwanturolan Muhammad Uba, ya ce adaddin kudin kayan da aka kama ya kai Nera biliyan biyu da miliyan dari biyar da hamsin da bakwai, baicin batun wata dabba da aka ce kudin fatunsu sun dara Nera biliyan biyu. Sun yi kamun ne daga daya zuwa tara ga wannan watan.

Kayan da aka kama sun hada da wasu motocin alfarma 16 da buhuhunan shinkafa 7200, wato kwatankwacin tirela goma sha biyu, sai kuma daskararun kaji katon kaji fiye da 1100. Akwai jarkokin mai fiye da 1300 da kayayyakin gwanjo da atanfofi.

Kwastan ta kama kayan ne saboda wai sun saba wa ka'idoji kana wasunsu ma sun karya doka ko kuma basu biya kudin fito ba.

An kama wasu buhuhuna 407 dake kunshe da fatun wata dabba mai suna Pongale a turance da nauyinsu ya kai kilo 1063 da ake niyar wucewa dasu kasar China. Kazalika an kama wani dan kasar China din a wani gida dake Ikeja, Lagos.

A saurari karin bayani a wannan rahoton na Babangida Jibrin

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwastan Ta Kama Kaya Da Kudinsu Ya Kusa Nera Biliyan Uku - 2' 59"