Hukumar Kwastam Za Ta Hada Gwiwa Da Manoma, Sauran Masu Ruwa Da Tsaki

Hukumar Kwastom

Hukumar kwastam ta bayyana hakan ne a wani taron karawa juna sani na yini biyu da ta shirya a birnin tarayya Abuja.

Hukumar hana fasakwabri ta kwastam a Najeriya ta bayyana cewa a shirye take tsaf ta hada gwiwa da manoma da sauran masu ruwa da tsaki a kasar, su yi aiki tare wajen aiwatar da sabuwar dokar hukumar ta shekarar 2023 don inganta yanayin samun kudadden shiga ga kasar da kuma kare manoman cikin gida wajen harkokin sayarwa da fitar da amfanin gonarsu a cikin gida da kasashen waje.

Hukumar Kwastom

Sabon mukaddashin babban kwanturola, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa da manoman kasar wajen tattara bayanan sirri na da manufar inganta ayyukan ta saboda idan aka kare manoma ana kare tattalin arzikin kasar ne.

Ya kara da cewa sabuwar dokar ta kwastam ta shekarar 2023 za ta taimaka matuka su rika sauke nauyin aikin da ya rataya a wuyansu sakamakon samar da tsauraran matakan hukunta masu karya doka ta yadda zai dakile aikata miyagun laifuka.

A.G Bashir Adeniyi

Babban daraktan cibiyar nazarin shari’a mai zurfi ta Najeriya, Farfesa Muhammad Tawfiq, na daga cikin mahalarta taron, inda ya yi bayani a kan yadda tsoffin dokokin hukumar kwastam suka hana ruwa gudu wajen ingancin aikin hukumar.

Ya ce sabuwar dokar ta shekarar 2023 da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu a kai za ta taimaka wajen kawar da wasu matsaloli da ake fuskanta, baya ga yadda za ta taimakawa manoma da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.

A nasa bangare, Malam Idris Giwa wanda ya wakilci babban sakataren ma’aikatar kudi da tsare-tsare ya ce sabuwar dokar za ta taimakawa gwamnati wajen samun karin kudadden shiga da taimakawa manoman cikin gida wajen fitar da kayayyakin su da kuma inganta aikin sa ido a yadda hukumar ke tafiyar da harkokinta.

Idan Ana iya tunawa, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya rattaba hannun a kan dokar a watan Afrilun shekarar 2023, dokar kwastam din da aka kwashe akalla shekaru 63 ba tare da yi mata wani gagarumin gyara ko sauyi ba.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwastam Zata Hada Gwiwa Da Manoma, Sauran Masu Ruwa Da Tsaki Wajen Inganta Aikinta