Hukumar Kwastam Tayi Kamen Haramtattun Kaya Na Fiye Da Miliyan 100

Hukumar Kwastam A Legas

Hukumar kwastan a Najeriya ta kama kayayyakin sumogal na fiye da Naira
miliyan 100 a birnin Legas, ciki kuwa harda kwayoyin Tramadol, tabar wiwi da kuma ganda ko bomo mai guba.

A hirar su da manema labarai a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin, Kwanturola mai kula da kan iyakar ta Seme, Muhammad Uba Garba yace
kayan da aka kama cikin kwanaki uku sun haura na naira miliyan 114, bayan haraji na naira biliyan 4 da rabi da hukumar ta samu daga watan Janairun banan zuwa Yuni.

Hukumar kwastan ba za ta gaji ba wajen yaki da 'yan fasa kwauri da kuma tattaro haraji wa kasa. Muhammad Garba, yayi tambaya don samun bayanin kan yarjejeniyar da gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu na kauda shingen kasuwanci, da yarda zai shafi harajin hukumar kwastam.

Sauran kayan da kwastam suka kama sun hada da shinkafa 'yar kasar waje, da kajin kankara na waje, da kuma motocin hawa. Sauran kayan sun hada da man girki da sukari, da kayan gwanjo na sakawa, sai kuma tabar wiwi, da naman bomo da aka hana anfani ko shigowa dashi, wanda ke haifar da cututtuka daban daban ga masu ci.

An hana cin naman bomon ko ganda, domin ana hada naman bomon da sinadaran ajiye gawa inji jami’in hukumar NAFDAC Dr. Nureeden Abdu, ya ce an dade da gwamnatin jihar legas ta fitar da gargadi ga masu cin ganda kamar yarda aka sanshi a wannan shiya ta Najeriya, dasu guji cin irin wannan ganda da ake shigowa da ita daga kasashen waje mai dauke da sinadaran hana gawa lalacewa.

Ga rahoton Babangida Jibrin cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwastan Ta Kama Kayan Sumoga FIye Da Miliyan 100