Hukumar Kwastam Ta Kama Bindigogi Sama Da 1000 a Legas

Wasu makamai da hkumar ta kama a baya cikin shekarar 2017

Hukumar kwastam ta ce ta kama makamai sama da 2000 cikin kasa watannin tara yayin da ake kokarin shiga da su cikin Najeriya daga kasashen waje.

Hukumar kwastam a Najeriya ta kama wasu makamai na bindigogi da yawansu ya kai 1,100, wadanda aka shigo da su cikin kasar ba bisa ka’ida ba.

Babban Comptroller Janar na hukumar ta kwastam, Janar Hameed Ali mai murabus ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce wannan shi ne karo na uku da ake kama makamai cikin kasa da makwanni tara.

Hukumar ta ce yanzu ta kama makamai da yawansu ya kai 2,201 a tsakanin wannan lokacin, kamar yadda wasu jaridun kasar suka ruwaito.

Masana harkar tsaro, irinsu Kanar Aminu Isa Kontagora mai murabus, suna ganin yanzu ne wannan lamari ke fitowa fili, amma dai an jima ana safarar muggan makamai a Najeriya.

“Muna fatan hukumar kwastam za ta bayyana mana mutanen da ke wannan mummunar sana’ar saboda mutane su farga.” Kanar Kontagora ya kara da cewa.

Ya zuwa yanzu an kama wani jami’i da ake bincike wanda shi ya taimaka aka fitar da kayan.

Saurari rahoton Babangida Jibril daga Legas domin jin karin bayani kan wannan rahoto:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwastam Ta Kama Bindigogi Sama Da 1000 a Legas - 3'02"