Har yanzu ana ci gaba da cece-kuce game da Majalisar Ministocin Najeriya.
Wannan kuwa yana zuwa ne tun daga lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya koma gida daga Ingila inda ya kwashe kwanaki masu yawa yana jinya.
Da yawan ‘yan Najeriya sun zura ido kuma sun kasa kunne suji yadda zata kaya a taron ministoci mai zuwa wanda aka saba yi ranar kowace ranar Laraba.
Wannan batun neman yin garanbawul ya kara fitowa fili ne bayan kalaman da ministar mata Aisha Jummai Alhassan tayi na jaddada goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria Alhaji Atiku Abubakar
Yanzu haka dai wannan kalamin Ministan Matan yana ci gaba da haifar da raayoyi mabanbanta a cikin kasa.
Ga Ibrahim Abdsulazeez da Karin bayani:
Facebook Forum