A wani taron manema labarai da hukumar ta Kwastam dake kula da iyakokin Najeriya, ta nuna cewa ana shigowa ne da tabar wiwi daga kasar Ghana. A cewar Alhaji Yusuf Umar dake zama kwantirola mai kula da shiyyar gabar ruwan yammacin Najeriya, yace a shekaran jiya ma sun kama wasu miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira Miliyan ‘daya da Talatin.
Hukumar kwastan ta bayyana cewa zata tashi tsaye wajen ganin ta kare kan iyakokin Najeriya, musamman ma ganin yadda ake zargin wasu ‘yan tsagera da neman tayar da rikici a kasar na ganin ba a ayi amfani da kan iyakokin Najeriya ba wajen shigowa da makamai kasar ba.
Shugaban hukumar kwastam mai kula da ruwan yammacin Najeriya, ya bayyana cewa nan gaba kadan za a samu wasu sabbin kayan aiki, da suka hada da jirage masu shawagi don taimakawa wajen yin sintiri a fadin kasar.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5