Hukumar Kwallon Kafar Najeriya Zata Taimakawa ‘Yan Kasar Da Kayan Abinci

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta ce zata taimaka wa ‘yan kasar da gudummowar kayan abinci a yayin da ake kokarin yaki da cutar coronavirus, shugaban hukumar Mr. Amaju Melvin Pinnick ne ya shaida hakan.

Mr. Pinnick ya ce hukumar tana bada tallafi sosai a bayan fage, tana kuma nuna wani hoton bidiyo game da cutar COVID-19 da ma’aikatar matasa da wasanni ta Najeriya ta saki.

A halin da ake ciki dai wasu yankunan Najeriya suna karkashin dokar ba shiga ba fita, a saboda haka hukumar zata taimaka da kayan abinci, ciki har da doya.

Jaridar Guardian ta fadi cewa wani jami’in hukumar kwallon kafar Najeriya ya ce kasar bata bukatar dan wasa Clemens Westerhoff dan kasar Dutch a matsayin kocin kungiyar kwallon kafar Super Eagles, wannan bayanin ya bayyana ne biyo bayan muhawara mai zafi dake gudana a tsakanin magoya bayan wasan kwallon kafa dake bayanin cewa Mr. Clemens Westerhoff ya bayyana sha’awar dawowa aikin horas da ‘yan wasan kwallon kafa.

Westerhoff shine ya jagoranci kungiyar kwallon kafar Najeriya da tayi nasara a kasar Tunisiya a shekarar 1994, a yayin da ya yi watsi da Super Eagles a gasar kwallon duniya da aka buga a Amurka a shekarar 1994, bayan da kasar Italiya ta sami nasara akan Najeriya a zagaye na biyu a gasar.

Sai dai kuma wata majiya daga hukumar kwallon kafar Najeriya na bayanin cewa, akwai kyakkyawar dangantaka a tsakanin hukumar kwallon kafar Najeriya da kuma mai horas da mata da ‘yan wasa a yanzu wato Mr. Gerno dan kasar Jamus wanda saura kiris a kammala batun sabunta kwantaragin sa.

A wani bangaren kuma mai yiwuwa ne hukumar kwallon kafar ta kammala shirye-shiryen amincewa da zaftare wani kaso daga cikin ‘yan wasan Super Eagles da kuma wasu ma’aikata a wani mataki na kawo sauki a sanadiyyar matsalar cutar COVID-19 da ta shafi fannin wasanni a fadin duniya.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwallon Kafar Najeriya Zata Taimakawa ‘Yan Kasar Da Kayan Abinci