Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Italiya Ta Dakatar Da Douglas Costa

Hukumar kwallon kafa ta kasar Itali ta dakatar da Douglas Costa, dan wasan kungiyar Juventus a wasanni hudu na Serie A, bayan wasansu da Sassuolo , a ranar Lahadi inda ta doke ta daci 2-1.

An sallami dan wasan dan kasar Brazil, mai shekaru 28, da haihuwa yayin wasan inda aka bashi Jan kati bayan da mataimakin alkalin wasa na VAR ya bayyanashi a TV karara yana tofa yawu a fuskar dan wasan Saussolo mai suna Federico Di Francesco.

Don haka bazai buga wasa da kungiyarsa zata yi da kungiyar Frosinone, Bologna, Napoli da kuma Udinese ba. Amman zai fafata a wasan da kulob din zai yi yau laraba a gasar zakarun nahiyar turai tsakaninta da Valencia.

Ku Duba Wannan Ma Ademola Lookman Ya Ce Ya Gwammace Takawa Najeriya Leda

Sai dai bayan tashi daga wasan Douglas Coast ya nemi afuwa daga wajan jagororin kungiyar da kuma magoya bayanta kan abun da tayi, sai dai hakan bai hana a hukunta shi ba.

Manchester City, ta ce ba ta riga ta fara tattaunawa da dan wasanta mai shekaru 23 a duniya ba mai suna Raheem Sterling ba, amma yanzu suna son yin tattaunawa akan mika tayinsu na yarjejeniyar da zata ƙare a shekara ta 2020.

An ambaci tsohon firaministan kasar Ingila Tony Blair a matsayin mai yiwuwa na gaba gaba cikin wadanda zasu zamo shugaba a bangaren gasar Premier League a wata tattaunawar da aka yi a cikin kwanan nan da kulob kulob masu buga gasar.

tsohon dan wasan Manchester United Dimitar Berbatov ya ce ya yi imanin cewa Juventus za iya kaiwa wasan karshe tsakanita da Manchester City ko Barcelona a gasar cin kofin zakarun Turai na bana.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Itali Ta Dakatar Da Douglas Costa 3' "20"