Hukumar dake kula da wasan kwallon kafa ta duniya (FIFA) a ranar Litinin ta turo wakilanta Messrs Luca Piazza da kuma Solomon Mudege a matsayin wadanda zasu sanya ido a zaben da za'ayi na shuwagabannin hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) wadda zasu ja ragamar hukumar daga shekara 2018 zuwa 2022.
A ranar Alhamis 20/9/2018 ne za'a gudanar da zaben a jihar Katsina dake tarayyar Najeriya inda ‘yan takara 24 a matakai daban daban zasu kara wajan neman jagorancin hukumar wadda suka hada tun daga matsayin Shugaban hukumar da kuma na kwamiti daban daban.
Cikin wadanda zasu fafata wajan takarar shugabanci sun hada da Amaju Pinnick wanda shine shugaban hukumar a yanzu haka da kuma tsohon shugabanta da ya yi a shekarun baya Aminu Maigari har ila yau akwai Taiwo Ogunjobi, wanda shima tsohon sakatarene a hukumar NNF sai kuma Chinedu Okoye mai kulob din Bimo Fc.
Dukkan mambobi 44 na hukumar kwallon kafa ta Najeriya za su jefa kuri'unsu a ranar Alhamis inda wasu masu jefa kuri'a za su isa Katsina ranar Talata kafin ranar zaben wasu kuwa tuni suka isa jihar Katsina.
Facebook Forum