Hukumar Kwallon Kafa Ta Ghana Ta Ja Kunnen Masu Harkokin Wasa A Kasar

Kungiyar Ghana Blackstar.

Hukumar kwallon kafar Ghana (GFA) ta yi gargadi ga klob klob da ‘yan wasa da alkalan wasa da jami’an kungiyoyin wasa da jami’an hukumar shirya wasanni das u daina shiga wasan dab a hukumar ce ta shirya shi ba.

Kungiyoyin wasan suna fara wasu wasannin zumunta a wani bangaren shirye shiryen fara kakar wasa ta gaba.

Amma ga dukkan alamu, ba hukumar kwallon kafa ta kasa c eta shirya wadannan wasannin ba kamar yanda ta fada a cikin kashedin nata.

A ranar Juma’a ce hukumar GFA ta fitar da wannan zazzafar kashedi ga kungiyoyin wasanni da ‘yan wasa da ma jami’ai das u guji haramtattun wasanni.

Sashin shirya wassnin lig din kasar a hukumar GFAta haramtawa duk masu ruwa da tsakin shiga irin wadannan wasa ko kuma wasan da wanda bashi da izinin hukumar ya shirya.

Suma alkalan wasa an gargadesu cewa kwamitin alkalai na karkashin rassan hukumar GFA a yankuna kadai ne suke da hurumin basu damar shiga tsakanin wasanni zumunuta ko wasanni da aka shirya a hukumance.