Hukumar Inganta Masana’antu Zata Inganta Rayuwar "Yan Najeriya

PLATEAU: Taron neman zaman lafiya tasaro da tattalin arziki

Hukumar inganta matsakanta da kananan masana’antu ta Najeriya ta lashi takobin samar da kwararru matakai da zasu inganta rayuwar al'umma.

A taron kwana uku da hukumar ta shiryawa manyan darektocinta da manyan ma’aikatanta, daga jihohi talatin da shida na fadin Najeriya, darektan hukumar Dikko Umaru Rada, yace sun shirya taron ne don samar da hanyoyin habbaka tattalin arzikin Najeriya.

Yace babu yadda za a yi tattalin arzikin Najeriya ya habaka, kasa ta ci gaba, idan ba a habaka masana’antu ba, yace mutanen da suka kawo gwamnatin bisa karagar mulki suna son suga tattalin arzikinsu ya ci gaba, suna kuma so suga masana’antunsu sun ci gaba.

Mallam Dikko Umaru Rada yace abinda shugaban kasa zai yiwa talaka kawai shine ya habbaka tattalin arziki da zai kai ga ci gaban kasa.

Shima a nasa bayanin gwamnan jihar Plato Simon Lalong yace yana da ikinin cewa taron zai inganta rayuwar al’umma musammam matasa wadanda suke da bukatar ayyukan yi

Ga cikakken rahoton Zainab Babaji, daga Jos, Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton taraon bunkasa masana'antun Najeriya-2:52"