Hukumar Hisba Ta Dauki Matakan Hana Bacewar Yara Da Shaye Shaye

A lokacin bukukuwan sallah karama lokaci ne da ake yawan samun bacewa ko satar yara mussaman ma lokutan hawan dawakai na sarki da mukarabansa ko a gidajen namun daji da filin shakatawa, a irin wadannan wurare ne ake samun afkuwar sata ko bacewar yara.

Akan haka ne DandalinVOA ya zanta da wasu iyaye dangane da irin shirin da zasu dauka na kare afkuwar batan yara, mal Maman ya ce yakan dauki yaransa da kansa misali gidan kakaninsu ko wuraren wasan yara da wajen kallon sarkin gudun kada a samu matsalar bacewar yara.

Akan haka ne muka leka hukumar hisbah ta jihar Kano muka kuma zanta da mataimakin kwamanda barista Nabahani Usman akan irin matakan da hukumar ta saka na kare bacewar yara, inda ya ce a dukkanin bukukuwan sallah suna sanya matakan tsaro na kare afkuwar hakan.

Daga karshe ya ce suna duba matsalolin shaye shaye, askin banza da matasa ke yi sannan sun sanya matakan kula da yara domin kai su wajen shakatawa inda ya bukaci iyayen yara su rubuta lambar waya su saka a al’jihun kowane karamin yaro domin magance bacewa.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Hisba Ta Dauki Matakan Hana Bacewar Yara Da Shaye Shaye