Daga shinkafa zuwa motoci, har yanzu gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakar kasa gaba daya. Masana tattalin arziki na nanata cewa, akwai bahaguwar dabara a matakin ko da kuwa hakan na kawowa gwamnatin makudan kudin shiga.
Masanan suna cewa rashin shirya kwararan matakai ta yadda rufe iyaka, ba zai kara jefa talakawa cikin tsananin kunci ba babbar matsala ce, alhali gwamnati na cewa ta na samun biliyoyin Naira kullum, wannan babban kalubale ne.
Hukumar ta kwastam na cewa matakin na samar da riba da ba a taba samu a tarihi ba, kuma hakan ya hana simoga, da dakile shigo da makamai ga 'yan ta'adda.
Yanzu dai dukkan kayan da aka hana shigowa da su ta kasa musamman motoci, a kan shigo da su ta teku daga jihar Legas kan haraji mai tsada, da ya tada farashin kayan da lamarin ya shafa.
Shugaban hukumar ta kwastam Kanar Hamid Ali ya ce a kan jingine duk wasu dokokin kare 'yanci in lamuran tsaro sun taso, a tabakinshi sai da kasar kafin a tada batun wani 'yanci.
A saurari cikakken rahoto daga sauti.
Your browser doesn’t support HTML5