Hukumar HALCIA Mai Yaki Da Cin Hanci A Nijer Ta Tashi Haikan Kan Batun Haraji

Mahamadou Issoufou

Hukumar yaki da cin hanci a jamhuriyar a Nijer ta bada sanarwar kwato wasu makudan kudaden haraji da suka makkkale a hannun wasu kamfanoni da masana’antun da ake zargi da turjewa ma’aikatar harajin kasar.

Daruruwan miliyoyin CFA ne shuwagabanin hukumar yaki da cin hanci wato HALCIA suka ce sun yi nasarar kwatowa daga kudaden harajin da suka makale a hannun wasu kamfanoni da masana’antu masu zaman kansu a shirin da hukumar ta kaddamar a ‘yan makwanin nan a wani lokacin da asusun gwamnatin kasar ke matukar bukatar kudade.

A cikin bayaninsa, mataimakin shugaban hukumar Salissou Oubandoma ya ce kamfanoni da dama ne aka gano biliyoyin kudi sun makale a hannun su, ma’aikatan haraji sun gaza karbo su, a dan haka ne hukumar yaki da cin hancin take dafawa masu karbar harajin da ma ma’aikatan kwastam baya domin zakulo hanyar da za a bi a kwato kudaden na gwamnati. Ya kuma ce kwalliya na biyan kudin sabulu a kan wannan yunkuri.

Bukin bayar da tallafin kudaden kungiyar Tarayyar Turai ga wasu kungiyoyi

Tunkaho da wasu dalilai irin na kulla mu’amula da masu fada aji da amfani da hanyoyin baiwa jami’an haraji cin hanci na daga cikin abubuwan da ake hasashen su ne suka janyo wannan matsala ta kin biyan kudaden haraji a nan Nijer lamarin da hukumar HALCIA tace ta dauri aniyar kawo karshensa.

Da yake bayyana ra’ayinsa a game da wannan yunkuri shugaban kungiyar ANLC reshen transparency International a Nijer Maman Wada ya jinjinawa hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA sannan ya bukaci shugabaninta su ci gaba da jajircewa don murkushe wannan mumunar dabi’a dake kokarin samun gindin zama.

Ya ce bai kamata a ce talaka na biyan haraji amma masu hannu da shuni na kauce wa biyan haraji ba saboda yin haka wani rashin adalci ne ga kasar. Ya kara da cewa babu mahalukin da yafi karfin doka, a dan haka hukumar HALCIA ta ci gaba da aiki na tabbatar da al’ummar kasar sun bada hakkin su ga kasa.

bikin-kaddamar-da-cibiyar-kasuwancin-albasa-a-nijar

A baya bayan na hukumar HALCIA ta karbi tallafin motoci da babura daga hannun kungiyar tarayyar turai a matsayin matakin karawa jami’anta azama sakamakon lura da irin nasarorin da hukumar ke samu wajen farautar mahandama dukiyar jama’a .

Ga rahoton wakilin muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijer Na DaukarMatakan Kwato Kudaden Haraji Da Karfi