Hukumar FBI Na Binciken Tashin Wuta a Wani Masallaci a Amurka

  • Ibrahim Garba

Shugaban Majalisar Tuntuba ta Musulmin Amurka (CAIR), na kasa Nihad Awad

Hukumar Bincike ta FBI ta yi tayin tukwicin dala dubu biyar ga duk wanda ya bayar da bayanin da ya taimaka wajen damke duk wanda ke da hannu a tashin wata wuta a wata cibiyar Islama da ke kudu maso gabashin Missouri, da ke nan Amurka a dadaidai lokacin da Musulmi ke shiga wata mai tsarki na Ramadan.

Jami’in tsaro na musamman mai kula da yankin St. Louis, shi ne ya bayyana wannan tayin a ranar Jumma’a, ‘yan sa’o’i da tashin wutar da asuba a Cibiyar Islama ta Cape Girardeau. Mutane tsakanin 12 zuwa 15 ne aka cetar ba tare da sun samu raunuka ba. Babban jami’in ‘yan kwana kwana Travis Hollis ya ce wutar ta yi matukar lalata ginin.

Shiyyar Missouri ta Majalisar Tuntuba ta Musulmin Amurka (CAIR a takaice), mai rajin kare muradun Musulmi, ta ce wutar ta fara tashi ne daga bakin kofar ginin. Kungiyar ta CAIR ta kula cewa akwai alaka tsakanin ranar da wutar ta tashi – ranar Alhamis, wacce ke jajeberin watan Ramadan, wata tsarki lokacin da Musulmi kan dukufa ga azumi da addu’o'i.